Yau Ake Fara Tattaunawar Sulhu Kan Rikicin Syria
https://parstoday.ir/ha/news/world-i2386-yau_ake_fara_tattaunawar_sulhu_kan_rikicin_syria
Yau Litinin ne wakilan bangarorin dake rikici a Syria ke fara tattaunawa a Geneva domin samun mafita a rikicin kasar da aka shafe shekaru shida ana yi.
(last modified 2018-08-22T06:57:58+00:00 )
Mar 14, 2016 03:01 UTC
  • tawagar wakilan gwamnatin Syria a Geneva
    tawagar wakilan gwamnatin Syria a Geneva

Yau Litinin ne wakilan bangarorin dake rikici a Syria ke fara tattaunawa a Geneva domin samun mafita a rikicin kasar da aka shafe shekaru shida ana yi.

tattaunawar wace ba tai kai tsaye ce ba ta hada wakilan 'yan adawa da kuma na gwamnati a shiga tsakanin MDD.

kafin hakan dai a jiyya Lahadi wakilin MDD a rikicin kasar Staffan de Mistura ya ce har yanzu dai akwai sabani tsakanin bangarorin biyu akan jadawalin tattaunawar.

babban sabanin dake akwai shi ne yadda 'yan adawan kasar ke son a dauko batun kujerar shugabancin kasar, yayin da bangaren gwamnati ke cewa batun kujera shugaba Bashar Al'Asad jan layi ne da ba za'a ketarewa ba.

Rikicin Syria wanda ya fara a shekara 2011, ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 270,000 yayin da rabin al'umma kasar suka kauracewa muhalen su saboda rikicin.