Kwamitin Tsaro Na MDD Zai Yi Zama Kan Batun 'Yan Rohingyas
A wani lokaci, yau Talata ne kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani zama domin tattauna batun 'yan Rohingyas.
Kwamitin ya amunce yin zamen ne bisa bukatar kasashen Birtaniya da kuma Suiden domin tattauna batun na musulmin Rohingyas a Myammar.
Wannan dai na zuwa ne bayan babban jami'in MDD mai kare hakkin bil adama, Zeid Ra'ad Al Hussein, ya danganta kisan da akewa musulmai 'yan kabilar Rohingya a kasar ta Myanmar da na kare-dangi.
A ranar Lahadi data gabata mayakan dake fafatukar kare 'yan Rohingyas sun sanar da tsagaita wuta, saidai gwamnatin Myammar ta ce bata tattaunawa da 'yan ta'adda.
A wata sanarwa data fitar gwamnatin ta Aung San Suu Kyi ta ce tana ci gaba da goyan bayan sojojin kasar, aman ta jaddada cewa sojojin sun samu umurninta na yin taka tsan-tsan da kuma kaucewa taba fararen hula a cikin aikinsu na tabbatar da tsaro.
Saidai kuma a wani labarin babban hafsan sojin kasar ta Myammar ya ce babu 'yan Rohingyas a cikin tarihin kasar.
Kawo yanzu alkalummen da MDD ta fitar sun nuna cewa adaddin 'yan gudun hijira Rohingyas da suka tsallaka zuwa Bnagaladash ya haura 300,000.