An Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zanga A Faransa
Dubban jama'a sun gudanar da zanga zanga a Paris domin nuna adawa da manufar shugaba Emmanuel Macron na yin garanbawul a fannin kwadago a kasar.
A jiya Talata, duban 'yan kasar faransa ne suka gudanar da gagarumar zanga-zanga domin nuna adawarsu da manufar kwadago ta shugaba Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya fuskanci kakkausar martani bayan da ya kira masu adawa da manufarsa ta garanbawul ga fannin kwadago da malalata, kalmar da ta tunzura dubban jama'a fitowa kan tituna domin nuna fushinsu.
'Yan siyasa da ke adawa da shugaban ciki har da Marine Le Pen sun yi amfani da wannan dama wajen mayar masa da martani da cewa ba ya kaunar Faransawa.
Jami'an 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar, sai dai a nasu bangare mahalarta zanga-zangar sun mayar da martani, inda suka dinga jifar 'yan sandar da duwatsu gami da wasu ababe masu tayar da hayaki.
Macron mai shekaru 39 da haihuwa wanda ya hau karagar mulki a watan Mayu, farin jininsa na ci gaba da kara yin kasa, inda masu sharhi ke danganta lamarin da gazawa da kuma kura-kurai ta fuskar siyasa.