Venezuella : An Kusa Cimma Matsaya Da 'Yan Adawa _ Maduro
(last modified Sat, 16 Sep 2017 05:17:48 GMT )
Sep 16, 2017 05:17 UTC
  • Venezuella : An Kusa Cimma Matsaya Da 'Yan Adawa _ Maduro

Shugaba Nicolas Maduro na Venezuella, ya tabbatar a Jiya Juma'a cewa, an kusa cimma yarjejeniya da 'yan adawa kan kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Mista Maduro ya ce sun yi nasara kaiwa ga zama teburin tattaunawa da 'yan adawa na kasar, wanda ya ce babban ci gaba a yunkurin samar da zamen lafiya a kasar.

A ranar Alhamis data gabata ne bangarorin biyu a shiga tsakanin kasar Dominique da MDD suka cimma matsaya ta hawa teburin tattaunawa a birnin Saint-Domingue domin kafa wani gungun kasashe aminnansu domin jagorantar zamen inda daga karshe suka amunce haduwa a ranar 27 ga watan Satumban nan domin tattaunawa.

Tunda farko dai 'yan adawan sun gindaye sharuda da suka hada da shirya zabuka ciki har da na shugaban kasa a karshen shekara 2018 da kuma sakin wasu fursunan siyasa 590, da dage takunkumin haramcin tsayawa takara da aka kakabawa wasu 'yan adawa.