Kasashe 7 Membobin Kwamitin Tsaro Sun Bukaci Bayani Kan Rikicin Myammar
https://parstoday.ir/ha/news/world-i24289-kasashe_7_membobin_kwamitin_tsaro_sun_bukaci_bayani_kan_rikicin_myammar
Kasashe bakwai membobin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci babban sakataren MDDn da ya gabatar musu da cikakken rahoto dangane da abubuwan da ke faruwa a kasar Myammar na irin kisan kiyashin da ake yi wa musulman Rohingya.
(last modified 2018-08-22T07:00:44+00:00 )
Sep 23, 2017 14:46 UTC
  • Kasashe 7 Membobin Kwamitin Tsaro Sun Bukaci Bayani Kan Rikicin Myammar

Kasashe bakwai membobin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci babban sakataren MDDn da ya gabatar musu da cikakken rahoto dangane da abubuwan da ke faruwa a kasar Myammar na irin kisan kiyashin da ake yi wa musulman Rohingya.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar a jiya Juma'a wasu kasashe guda bakwai membobi a kwamitin tsaron MDD cikin wata wasika da suka rubutawa babban sakataren MDDn Antonio Guterres sun bukace su da ya gabatar musu da rahoto dangane da rikicin da ke faruwa a kasar Myammar.

Rahotannin sun ce kasashe bakwai din sun haka da Sweden, Amurka, Birtaniya, Faransa, Masar, Senegal da Kazakhstan.

Kafin hakan ma dai babban sakataren MDD ya bayyana irin kisan gillan da ake yi wa musulmin Rohingya a matsayin kisan kiyashi da nufin kawo karshen wata al'umma. Shi ma kwamitin tsaron a cikin wata sanarwa da ya fitar ya yi Allah wadai da kisan gillan da ake yi wa musulmin da kuma kawo karshen hakan.