MDD : Kwamitin Sulhu Zai Saurari Kofi Anan Kan Batun Myanmar
(last modified Fri, 13 Oct 2017 05:52:12 GMT )
Oct 13, 2017 05:52 UTC
  • MDD : Kwamitin Sulhu Zai Saurari Kofi Anan Kan Batun Myanmar

A wani lokaci nan gaba ne ake sa ran kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani zama na musamen kan batun kasar Myanmar.

A zaman na yau Juma'a kwamitin dai zai saurari tsohon Sakatare Janar na MDD, Kofi Annan kan halin da 'Yan kabilar Rohingya a Myanmar ke ciki.

Kasashen Faransa da Burtaniya ne suka bukaci gudanar da taron da Annan yayin da Majalisar ke nazari kan irin matakan dauka kan halin da musulmin na Rohingya ke ciki.

A kwanan baya dai hukumar kare hakkin bil- adama ta Majalisar ta zargi  sojojin Myanmar da yunkurin share wata kabila daga doron kasa.

A halin da ake ciki dai kungiyar kasashen Turai na shirin katse duk wata hulda da kasar ta Myanmar.