Hukumar WHO Ta Yi Gargadin Dangane Da Yaduwar Cutar Zika
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta nuna damuwarta dangane da yiyuwar ci gaba da yaduwar cutar nan ta Zika da ta bullo zuwa yankuna daban daban na duniya ciki kuwa har da nahiyoyin Afrika da Asiya da aka fi samun yawan haihuwa a can.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar hukumar lafiya ta duniyar ta bayyana wannan damuwar ne bayan wasu rahotanni da suke nuni da cewa an fara samuwar yaduwar cutar ta hanyar jima'i a Amurka inda ta bukaci da a gudanar da bincike kan wannan rahoton.
A shekaran jiya Talata ce dai mahukunta a jihar Texas ta Amurka suka sanar da cewa an bayyanar kamuwa da cutar ta Zika ta jihar ta hanyar jima'i, wanda hakan shi ne karon farko da aka samu wani ya kamu da cutar ta wannan hanya, lamarin da ya sanya hukumar ta WHO cikin damuwa kan yiyuwar ci gaba da samun yaduwar cutar.
Ita dai wannan cutar ta Zika wadda sauro ke yada kwayarta tana haddasa haihuwar jarirai da matsalar kwakwalwa ko kuma kananan kawuna yayin haihuwarsu, ya zuwa yanzu ta shafi dubban jarirai a kasar Brazil lamarin da ya sanya hukumar ta WHO sanar da dokar ta baci da kuma kiran da a yi taka tsantsan da cutar.