MDD Ta Bukaci A Tallafawa Kungiyar G5 Na Sahel
https://parstoday.ir/ha/news/world-i25004-mdd_ta_bukaci_a_tallafawa_kungiyar_g5_na_sahel
Babban sakataren majalisar dinkin duniya António Guterres ya bukaci kasashen duniya su tallafawa kungiyar kasashen G5 ta yankin sahel a tsakiyar Afrika
(last modified 2018-08-22T11:30:51+00:00 )
Oct 17, 2017 19:04 UTC
  • MDD Ta Bukaci A Tallafawa Kungiyar G5 Na Sahel

Babban sakataren majalisar dinkin duniya António Guterres ya bukaci kasashen duniya su tallafawa kungiyar kasashen G5 ta yankin sahel a tsakiyar Afrika

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar faransa ya nakalto António Guterres yana fadar haka a jiya litinin a lokacin da yake gabatar da wani rahoto a gaban komitin tsaro na majalisar. Guterres ya kuma kara da cewa a halin yanzu yankin Sahel yana fama da matsaloli masu yawa wadanda suka hada da sauyin yanayi da kuma tsaro. 

Babban sakatarin ya kara da cewa wadan nan kasashen biyar wato Mauritania, Chadi, Niger, Borkina faso da kuma Mali suna fama da matsalolin tsaro masu yawa wadanda suka kaisu ga kafa rundunar sojoji mai mayaka 5000, amma rundunar bata da  isassun kayakin aiki da kuma kudade don ganin sojojin sun fara aikin dawo da zaman lafiya a yankin.

Kungiyar tana bukatar tallafin kayan aiki da kuma kudade don ganin wannan gagarumin shirin ya fara tafiya kamar yadda ake so inji shi.