Qatar Ta Cimma Yarjejeniyar Tsaro Da Rasha
Oct 26, 2017 11:20 UTC
Kasashen Rasha da Qatar sun cimma yarjejeniyar tsaro tsakaninsu a wata ziyara da ministan tsaron Rasha Sergueï Choïgou, ya kai a birnin Doha.
Wata sanarwa da hukumomin Qatar suka fitar ta ce an cimma yarjejeniyar ce a jiya Laraba bayan tattaunawa tsakanin ministan tsaron Rasha da Sarkin Qatar din Sheikh Tamim ben Hamad Al-Thani.
Wannan dai ita ce ziyara irinta ta farko da wani ministan tsaron Rasha ya kai a Qatar.
Yarjejeniyar da ministocin tsaron kasashen biyu suka sanya wa hannu ta kunshi cinikan makamai na kariya hare-haren sama da kuma kayan soji.
Wannan dai ita yarjejeniya ta baya baya da Qatar ta cimmawa da wata kasa tun bayan da Saudiyya da makoftanta suka katse hulda da ita.
Tags