Harin Khan Cheikhoun : Akwai Sabani A Rahoton MDD_Rasha
Oct 27, 2017 06:03 UTC
Kasar Rasha ta kalubalanci rahoton MDD wanda ya nuna karara cewa gwamnati Siriya ce take da hannu a harin da aka kai da makami mai guba a lardin Khan Cheikhoun.
Harin wanda aka kai a ranar 4 ga watan Afrilun da ya gabata ya dai yi sanadin mutuwar mutane sama 80 ciki har da yara a lardin na Khan Cheikhoun dake yankin Idleb a arewacin kasar Siriya.
A cewar Rasha rahoton wanda kwararun MDD suka gabatar yana cike da sabani, na abubuwan da basu tafiya daidai da bayanai marasa tushe wanda kuma ba'a tabbatar da su ba; kamar yadda mataimakin ministan harkokin wajen Rashar Sergueï Riabkov ya sanarwa kamfanin dilancin labaren Interfax.
Tags