An Tarwatsa Helkwatar Kungiyar Daesh (ISIS) A Gabashin Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i25295-an_tarwatsa_helkwatar_kungiyar_daesh_(isis)_a_gabashin_siriya
Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar tarwatsa helkwatar dakarun kungiyar ta'addancin nan ta Daesh (ISIS) da ke gabashin kasar Siriya a ci gaba da fada da kungiyar da ake yi a kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:56+00:00 )
Nov 03, 2017 02:23 UTC
  • An Tarwatsa Helkwatar Kungiyar Daesh (ISIS) A Gabashin Siriya

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar tarwatsa helkwatar dakarun kungiyar ta'addancin nan ta Daesh (ISIS) da ke gabashin kasar Siriya a ci gaba da fada da kungiyar da ake yi a kasar.

Kafar watsa labaran Sputnik na kasar Rashan ta bayyana cewar a cikin wata sanarwa da ta fita, Ma'aikatar tsaron kasar Rashan ta bayyana cewar cikin kwanaki biyun da suka gabata jiragen yakin kasar sun yi ruwan bama-bamai a cibiyoyi da sansanonin kungiyar ta'addancin nan ta Daesh da ke lardin Deir al-Zur.

Sanarwar ta kara da cewa a yayin wadannan hare-hare an sami nasarar tarwatsa helkwata da kuma wasu sansanonin na kungiyar ta'addancin da ke garin Al-Bukamal. Kamar yadda kuma an kai hare-haren kan taron dakarun kungiyar ta Daesh da kuma wasu rumbunansu na makamai.

Sojojin Siriya da suke samun goyon bayan sojoji da jiragen yakin Rashan sun sami nasarar kwato yankuna da dama daga hannun 'yan ta'addan na Daesh da suke rike da su a baya.