Majalisar Dokokin Kasar Holland Ta Haramta Sayar Wa Saudiyya Da Makamai
Majalisar dokokin kasar Holland ta amince da wata doka da aka gabatar mata na haramta wa sayarwa da kuma aikewa da makamai zuwa kasar Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar majalisar dokokin kasar Holland, a zaman da ta yi a jiya Talata, ta haramta wa gwamnatin kasar sayar da makamai ko kuma aikewa da su ga gwamnatin kasar Saudiyya saboda ci gaba take hakkokin bil'adama da take yi a kasar Yemen.
Kamfanin dillancin labaran na Reuters ya kara da cewa majalisar dokokin kasar Holland ta amince da wannan doka ne don karfafa matsayar da majalisar kasashen Turai ta dauka a watan Fabrairun da ya gabata inda ta bukaci kasashen Birtaniyya, Faransa da sauran kasashen Kungiyar Tarayyar Turai din da su dakatar da sayar da makamai ga kasashen da suke kai hari kan fararen hula a kasar Yemen.
Kimanin shekara guda kenan Saudiyya da kawayenta suke ci gaba da zubar da jinin al'ummar Yemen da ba su ci ba su sha ba, lamarin da ke ci gaba da fuskantar tofin Allah tsine daga bangarori daban-daban na duniya.