Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Alkawalin Kare Muhalli
Babbana magatakardar Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya ce; Kare muhalli yana a matsayin ginshikin zaman lafiya, tsaro da kuma ci gaba.
Antonio Gutters ya bayyana haka ne a cikin sakon da ya aike a yau 6 ga watan Nuwamba wacce ita ce ranar duniya ta kare muhalli. António Guterres ya kuma bayyana damuwa matuka akan illar da yaki yake haddasawa ga muhalli sannan ya kara da cewa; Yaki yana yin illa matuka ga harkokin ci gaba da kuma muhalli.
Bugu da kari, babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar ya ce; Illar da muhalli zai samu zai yi tasiri na lokaci mai tsawo ga mutane.
A karshe babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga al'ummar duniya da ta yi kokarin rage illar da yaki yake yi ga muhalli da kuma kare dabi'a domin samun ci gaba mai dorewa.