MDD Na Kara Matsin Lamba Ga Gwamnatin Myanmar Kan 'Yan Rohingya
Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya kira gwamnatin Myanmar data kawo karshen aikin sojinta a yankin Rakhine da kuma baiwa daruruwan musulmin Rohingya dake gudun hijira a kasar Bangaladash damar komawa gida.
Kimanin 'yan gudun hijira Rohingya dubu dari tara ne ke yashe a cikin yanayi rayuwa marar kyau a karkashin tantunan da ake kebe masu a kudancin Bangaladash.
Tun da farko dai majalisar dinkin duniya ta danganta lamarin da yunkurin share wata kabila a doron kasa.
A cikin sanarwar da kasashe mambobin kwamitin sulhu suka fitar a jiya sun yi tir da rikicin da ya cilastawa tsirarun 'yan Rohingya barin muhallensu.
Haka zalika kuma mambobin sun nuna matukar damuwarsu akan irin cin zarafi, kisa, fyade da kone-konen gidajen 'yan Rohingyas suka gani a tsawan wannan lokaci, tare da bukatar a gurfanar da duk wani hannu a cikin wannan lamari.