Amurka / Sin : Akwai Mafita A Rikicin Koriya Ta Arewa_Trump
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce yana da yakini akan samun mafita kan rikicin Koriya ta Arewa.
Trump, wanda ke bayyana hakan a birnin Pekin a yayin ganawa da twakaransa na China ko Sin, Xi Jinping, ya ce mun yi tattaunawa mai kyawo kan batun Koriya ta Arewa, kuma ian tsammani kamar ku da akwai mafita kan batun Koriya ta Arewa.
A shekara guda cif da zabensa a matsayin shugaban Amurka, Donald Trump ya isa kasar China a ci gaba da ran- gadin da ya ke a wasu kasashen Asiya.
Hulda tsakanin mayan kasashen duniyar biyu, babu tamakar ta a cewar shugaba Jinping.
Kasar China dake da ke tafiyar da illahirin harkokin kasuwancin da Koriya ta Arewa, na da mahimmiyar rawa da za ta taka wajen matsin lamba wa gwamnatin Kim Jong-Un da ta yi wani gwajin makamin nukiliya a watan Satumba da ya gabata.