Jan Kunan MDD Game Da Cin Zarafi A Kasar D/Congo
Majalisar Dinkin Duniya ta yi hannunka mai sanda ga hukumomin kasar D/ Cango kan duk wani mataki na cin zarafin jama'a yayin babbar zanga-zangar da 'yan adawa suka kira ta ranar Laraba 15 ga watan Nuwamba.
'Yan adawan kasar ta congo dai sun kira zanga-zangar ce a ranar Labara 15 ga watan nan na Nuwamba a fadin kasar domin nuna adawarsu ga sabon jaddawalin zabukan kasar da aka fitar, wanda kuma ya kara wa'adin zaman shugaba Joseph Kabila a kan karagar mulki har ya zuwa watan Janairu na 2019.
Dangane da nauyin da ya rataya a kanshi na rashin tsoma baki a cikin lamurra na kasar ta congo, ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta congo MONUSCO ya ce zai bi lamarin sau da kafa, kuma zai sanar da duk wani yanayi na cin zarafi bil-Adama a cewar Maman Sidikou babban wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta congo, inda ya yi kira ga hukumomin da su yi biyayya ga hakkokin jama'a musamman ma kan incin yin taruka, ko zanga-zanga dai dai yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Sau tari jami'an tsaro a kasar ta Congo kan cin zarafin masu zanga-zanga, kaman yadda ya gudana yau da wata guda a birnin Goma da ke gabashin kasar, inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.