Rasha / Siriya : Putin Ya Gana Da Assad A Sotchi
Nov 21, 2017 10:56 UTC
Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya gana da takwaransa na Siriya Bashar Al Assad a birnin Sotchi da ke kudu maso gabashin Rasha.
A yayin ganawar shugaba Putin ya jinjinawa Assad kan nasara da ya samu wajen yaki da ta'addanci.
Putin ya kuma sanar da Assad cewa zai tattauna ta wayar tarho a yau Talata da shugaba Trump na Amurka kan halin da ake ciki a Siriya.
Wannan ganawar dai na zuwa ne kwamaki biyu kafin babban taron kasashen Rasha, Iran da Turkiyya na neman samun mafita ta siyasa don magance rikicin da aka kwashe shekaru shida ana yi a kasar ta Siriya.
Tags