Sudan Ta Nemi Taimakon Rasha Kan Bakar Siyasar Amurka
Shugaba Omar El-Bashir na Sudan wanda kotun hukunta mayan laifuka ta duniya ICC ke nema ruwa a jallo ya fara wata ziyara ta kwanaki hudu a kasar Rasha, mai manufar karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.
A yayin ganawarsa da shugaba Vladimir Putin na Rashar, a birnin Sotchi, Al-bashir ya bayyana cewa kasarsa na bukatar goyan bayan sauren kasashe kan miyagun manufofin Amurka.
Shafin yada labarai na Press TV wanda ya rawaito labarin ya ce, Sudan tana adawa da shishigi na gwamnatin Washington, wadanda su ne ummul aba'isin tashe-tashen hankulan dake faruwa a yankin a cewar shugaba Al-Bashir.
A daya bangare kuwa da ya tabo batun Siriya, Al-Bashir ya ce samun zaman lafiya ba zai taba yiwuwa ba ba tare da Bashar Al Assad ba, tare da jaddada wajabcin yin hadin gwiwa na tsakanin kasashen biyu kan batun kasar ta Siriya.
Omar Al-bashir ya kuma ce sun tattauna da ministan tsaron Rasha kan batutuwan da suka shafi harkokin soji na kasashen biyu.