Nov 29, 2017 12:16 UTC
  • Myanmar: Paparom Ya Gana Da   Aung San Suu

A jiya talata ne aka yi ganawar tsakanin babban limamin darikar roman katolika da kuma shugabar gwamnatin Myanmar a birnin Rangon.

Ganawar bangarorin biyu ta dauki mintoci 45 inda suka tattauna batun matsalar musulmin Rohinga dubu 620 da suke gudun hijira.

Paparoman ya fara ziyara ne a kasar Myanmar tun a ranar litinin, inda aka yi masa kyakkyawar tarba a babban birnin kasar Rangon.

Daga cikin wadanda paparoman ya gana da su, da akwai babban kwamandan sojan kasar Janar Min Aung Hiling wanda ya riya cewa; Babu banbancin addini a kasarsa."

 Janar din dai yana kokarin kore cutar da al'ummar Rohinga ne da gwamnatin kasar ta yi tare da mabiya addinin Buddha.

An kone musulmin da dama da kuma gidajensu da goninsu, tare da korar wasu dubbai zuwa waje.

 

Tags