Taron Gaggawa Kan Bautar Da Bakin Haure A Libiya
Kasashen Faransa, Nijar da Chadi, da MDD da kungiyoyin EU da AU zasu gudanaar da wani taron gaggawa kan batun bautar da bakin haure a Libiya a daura da taron koli na tarayya Turai da AFrika a birnin Abdijan na kasar Ivory Coast.
Fadar shugaban kasar Faransa wacceta fitar da labarin ta ce Emanuelle Macron zai gana da bangarorin a wani taron gaggawa akan batun cinikin bakin haure tamakar bayi a Libiya.
Ko baya ga wadannan bangarorin shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ita ma zata halarci tattaunawar.
Ganawar dai ta biyo bayan bukatar da Emanuelle Macron na Faransa ya gabatar a cikin wani jawabinsa a jiya a birnin Ouagadugu an Burkina Faso kan daukar mataki akan masu safara bakin haure.
Kafin hakan dama shugabannin AFrika da dama kamar Isufu Mahamadu na Jamhuriya NIjar ya bukaci takwaransa na Ivory Coast Alhassan Watara da ya saka batu a cikin ajandar taron kolin na EU da AU dake gudana yanzu haka a birnin Abidjan, tare kuma da bukatar kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC data binciki batun.