Rasha Ta Zargi 'Yan Tawayen Siriya Da Rusa Zaman Ganeva
Gwamnatin Rasha ta ce 'yan adawa ne suka kawo cikas a tattaunawar Ganeva game da makomar Siriya
Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harakokin wajen Rasha ta fitar, ta ce bangaren 'yan adawa sun sanya tarnaki a yayin da aka fara tattaunar sulhu na birnin Ganeva da gangan domin kada a gudanar da zaman da za a yi a birnin Sochi na kasar Rasha.
har ila yau ma'aikatar harakokin wajen ta Rasha ta ce zarge-zange da mahukuntan Amurka ke yi kan Rasha a game da karya yarjejeniyar makamai, zargi ne da ba shi da wani tushe.
Har ila yau Rashan ta bayyana cewa tarin makaman da Amurka ke turawa zuwa kasar Ukraine, wani lamari ne da ke bayar da karfin gwiwa ga gwanatin Ukraine na ci gaba da zubar da jini a gabashin kasar.