MDD Za Ta Dakatar Da Ma'aikatan Ta 131.
https://parstoday.ir/ha/news/world-i26765-mdd_za_ta_dakatar_da_ma'aikatan_ta_131.
Kakakin Saktare Janar na MDD ya bayyana cewa, Majalisar za ta dakatar da ma'aikatanta 131 saboda ta rage kudaden da take kashewa
(last modified 2018-08-22T07:01:12+00:00 )
Dec 27, 2017 14:44 UTC
  • MDD Za Ta Dakatar Da Ma'aikatan Ta 131.

Kakakin Saktare Janar na MDD ya bayyana cewa, Majalisar za ta dakatar da ma'aikatanta 131 saboda ta rage kudaden da take kashewa

Stephen Dow Jaryk kakakin saktare janar na Majalisar dinkin Duniya ya ce Majalisar ta dauki rage ma'aikatan ta zuwa 9959.kafin hakan dai wakiliyar Amurka a MDD Nikki Haley Amurka dake a matsayin kasar farko na samar da bajat din Majalisar dinkin Duniya ta daukin kudirin rage kudaden da take bawa Majalisar da dala miliyan 285.

Nikki Haley ta ce duk da irin makudan kudin da ake bawa Majalisar dinkin Duniya, amma ba ta yin aikin da ya kamata ta yi.

Wannan mataki da Amurka ta dauka na zuwa ne bayan kashin da ta sha a zauren Majalisar Dinkin Duniya na watsi da kudirin shugaba Trump na ayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin Haramtacciyar kasar Isra'ila duk kuwa da irin barazanar da ta yi kafin gudanar da zaben.