Tarayyar Turai Ta Amince Da Kakabawa Kasar Venezuela Takunkumi.
Kasashen Turai sun amin ce su dorawa wasu manya manyan jami'an gwamnatinn kasar Venezuela takunkuman tattalin arziki saboda murkushe yan adawa da gwamnatin kasar take yi.
kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya bayyana cew a yau Alhamis ne tarayyar turai ta bayyana amince da dorawa manya manyan mutane na kasar Venezuela su 7 tankunkumi, inda zasu rufe asusun ajiyar kudadensu a kasashen sannan zasu hana su Visar shiga kasashen.
Gwamnatin kasar Amurka da kuma kasashen na turai suna goyon bayan yan adawa da gwamnatin kasar ta Venezuela a ricikin da ya barke a cikin shekarar da ta gabata.
gwamnatin kasar Venezueala dai tace tana kokarin kyautata tattalin arzikin kasar wanda ya tabarbare sanadiyyar faduwar farashin danyen man fetur a kasuwannin duniya. Sai dai yan adawar kasar sun dauki matsin tattalin arzikin da kasar ta fada ciki a matsayin makami na yakar gwamnatin shugaba Nicolás Maduro.