An Cimma Yarjejjeniyar Aiki Tare Tsakanin Rasha Da EU
(last modified Sat, 20 Jan 2018 11:50:02 GMT )
Jan 20, 2018 11:50 UTC
  • An Cimma Yarjejjeniyar Aiki Tare Tsakanin Rasha Da EU

Kasar Rasha ta cimma yarjejjeniya tare da kungiyar tarayyar Turai wajen zuba hannun jari da kuma aiki tare a kan iyakokinsu.

Ma'aikatar tattalin arzikin kasar Rasha ta sanar a jiya juma'a cewa kasar ta cimma yarjejjeniya tare da kungiyar tarayyar Turai kan zuba hannayen jari a kasashensu tare kuma da gabatar da wani shiri na aiki tare a kan iyakokin kasar da kasar Lithuania, da kuma kasar Poland.

Manufar wannan yarjejjeniya dai shi ne, kare wuraren tarihi da al'adu,kare muhalli, tabbatar da tsaro a kan iyakokin kasashen da kuma bunkasa sufuri da kai kawo a tsakanin kasashen.

Sanarwar ta tabbatar da cewa sabuwar yarjejjeniyar ta kara yawan ayyuka guda 7 da za a yi a tsakanin bangarorin biyu, inda aka kiyasta cewa zai lakume tsabar kudi har Euro miliyan 86 da dubu 900 a bangaren tarayyar Turai, sannan kuma a bangaren kasar Rasha Euro miliyan 51 da dubu 200.