Siriya : Faransa Ta Sanya Takunkumi Kan Wasu Kamfanoni Da Jami'ai 25
Kasar Faransa ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu Cibiyoyi da jami'ai su 25 kan zargin taimakawa shirin Siriya na sarafawa da kuma kera makamai masu guba.
Daga cikin kamfanonin da takunkumin ya shafa har da na kasar ta Faransa da na Labanon da kuma China galibi masu sarafa kayan wutar lantarki, wadanda ke da cibiyoyi a birnin Beyrout.
Babu dai wani jami'i a cikin gwamnatin Siriya da takunkumin ya shafa kawo yanzu, kasancewar babu kwararen hujoji akansu a cewar sanarwar da hukumomin Faransa suka fitar.
Wannan matakin dai na zuwa ne a yayin da Faransar ke karbar wani taro yau a birnin Paris wanda sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, ke halarta domin daukar mataki kan duk wani mahaluki dake da hannu a zargin amfani da makami mai guba na baya baya nan a yankin Ghouta dake gabashin birnin Damascos na Siriya.