Rasha Na Karbar Bakuncin Taron Tattaunawa Tsakanin 'Yan Siriya
Yau Talata, ake fara wani taron tattaunawa tsakanin 'yan Siriya a birnin Sotchi na kasar Rasha.
Fadar gwamnnatin Rasha ta ce wakilai daga bangarori daban daban ciki har da 'yan siyasa da kungiyoyin farar hula na Siriya kimanin 1,500 zasu halarci taron.
Rasha dai ce ta shirya taron tare da hadin gwiwar hukumomin Iran da Ankara, da nufin samar da wani sabon kundin tsarin mulki ga kasar ta Siriya.
Sai dai gamayar manyan jam'iyyun adawa na Siriya (CNS) sun sanar da kin halartar taron bayan kasa cimma wata matsaya a zaman tattaunawa kan rikicin kasar ta Siriya a Vianna a shiga tsakanin MDD.
A yayin da su kuwa bangaren Kurdawa suka ki amsa gayyatar taron saboda farmakin da Turkiyya ke kaiwa a yankin Afrin.
Kasashen Amurka da Faransa ma sun ce ba zasu aike da wakilai a taron ba, saboda fargabar kada ya yi katsin landan ga tattaunawar da ake a shiga tsakanin MDD, koda yake babban sakatare na MDD ya aike da wakilinsa na musaman kan rikicin kasar ta Siriya, Staffan de Mistura.