Venezuella : Maduro Zai Yi Takara A Zabe Mai Zuwa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i27887-venezuella_maduro_zai_yi_takara_a_zabe_mai_zuwa
Jam'iyya mai mulki a Venezuella, ta tsaida shugaban kasar mai ci, Nicolas Maduro a matsayin dan takarar ta a zaben shugaban kasar na kafin wa'adi dake tafe.
(last modified 2018-08-22T11:31:22+00:00 )
Feb 03, 2018 06:27 UTC
  • Venezuella : Maduro Zai Yi Takara A Zabe Mai Zuwa

Jam'iyya mai mulki a Venezuella, ta tsaida shugaban kasar mai ci, Nicolas Maduro a matsayin dan takarar ta a zaben shugaban kasar na kafin wa'adi dake tafe.

A karshen watan Afrilu mai na wannan shekara ne aka shirya gudanar da zaben na kafin wa'adi a wannan kasa dake fama da matsalar tattalin arziki.

A wani taron siyasa da jam'iyyar mai mulki a venezuela ta (PSUV), ta gudanar a jiya Juma'a ta sanar da tsaida shugaba Maduro a zaben.

Mista Maduro ya bayyana a wurin taron cewa suna kan yin babbar nasara a zaben, tare da yin kakkausar suka ga wasu kasashen yamma musaman Amurka wacce ya zarga da yunkurin tada fitina a kasar a koda yaushe.