Kudirin Kwamitin Tsaron MDD Karo Na 30 Kan Rikicin Kasar Siriya
(last modified Mon, 26 Feb 2018 05:54:55 GMT )
Feb 26, 2018 05:54 UTC
  • Kudirin Kwamitin Tsaron MDD Karo Na 30 Kan Rikicin Kasar Siriya

A Daren Asabar din da ta gabata, kwamitin tsaron MDD ya aminici da wani kudiri mai lamba 2401 kan rikicin kasar Siriya wanda ya samu amincewar dukkanin manbobin kwamitin 15.

Wannan sabon kudiri da kasashen Kuweit da Sweden suka gabatar da shi, ya kumshi tsagaita wuta na tsahon kwanaki 30a wuraren da aka killace 'yan ta'adda a Syria musamman yankin Gouta da ke gabashin birnin Damascus , kuma dukkanin mambobin kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ne suka amince da kudirin, bayan kwashe tsawon kwanaki ana tafka muhawara a kansa.

Tsawon makonnin da suka gabata, 'yan ta'addan Jabhat Nusra da ke samun goyon baya da dauki daga kasashen Amurka, Saudiyya da kuma Isra'ila, da suka kafa sansaninsu a yankin Gouta da ke gabashin birnin Damascus, sun ta harba daruruwan makaman roka a kan birnin na Damascus, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama, wanda hakan yasa ala tilas dakarun na Syria daukar matakan murkushe 'yan ta'addan.

A ranar lahadi na makun da ya gabata ce, dakarun na siriya suka fara kai farmaki na murkushe 'yan ta'addar, amma tun daga wannan Rana,muryar kasashen Yamma da Amurka ta fara ta shi bisa da'awar a bawa kungiyoyin agaji damar da shigar da taimako a yankin, kamar yadda suka saba cikin shekaru 7, kasashen yamma da Amurka sun yi ta farfaganda a kan gwamnatin Siriya tare da kai kawo zauren MDD na ganin an dakatar da wannan farmaki. kafin kudirin ya samu amincewa an samu sabani mai tsanani a tsakanin masu goyon bayan gwamnatin ta Siriya da masu goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'addar.

Jakadan Syria a majalisar dinkin duniya Bashar Jaafari ya bayyana cewa, gwamnatin Syria za ta mutunta wannan kudiri, amma hakan ba zai shafi 'yan ta'addan ISIS, da Jabhat Nusra ba, inda ya ce gwamnatin Syria ba zata taba dakatar da yaki da wadannan kungiyoyin ba har sai an murkushe su.

Saidai a nasu bangaren kasashen dake goyon bayan 'yan ta'adda na kokarin alakanta wannan farmaki da tattaunawar sulhun da ake yi a tsakanin 'yan kasar ta Siriya, Heather Nauert kakakin ma'aikatar harakokin wajen Amurka ta bayyana cewa harin Couta alama ce na wargaza tattaunawar sulhun da ake yi a tsakanin 'yan kasar ta Siriya.

Masana harakokin siyasa da tsaro na yankin gabas ta tsakiya sun bayyana cewa ware kungiyoyin 'yan ta'adda irin su Alka'ida, Jabhatu-Nusra,da ISIS, nasara ce ga jami'an Diplomasiyar kawacen siriya kamar Rasha da Iran.

Don haka ana iya bayyana cewa wannan kudiri mai 2401, nasara ce ga gwamnatin kasar Siriya, ganin cewa ba haka, magoya bayan  kungiyoyin 'yan ta'addar suka so ba, kuma kamar yadda Mansoor Ayad Atiyi wakilin kasar Kuweit a zauren MDD ya tabbatar, wannan kudiri, zai magance matsala ce ta ficin gadi, ba ta dindin din ba.