Kotun ICC Ta Daure Tsohon Shugaban Sabiyawa, Karadzic Shekaru 40
(last modified Fri, 25 Mar 2016 04:53:39 GMT )
Mar 25, 2016 04:53 UTC
  • Kotun ICC Ta Daure Tsohon Shugaban Sabiyawa, Karadzic Shekaru 40

Kotun duniya mai shari'ar manyan laifukan yaki ta yanke wa tsohon shugaban Sabiyawan Bosniya Radovan Karadzic hukunci daurin shekaru 40 a gidan yari saboda samunsa da hannu dumu dumu cikin kisan kiyashi da aka yi wa wasu musulmai yanki Srebrenica a shekarar 1995.

Yayin da yake sanar da hukumci, babban alkalin kotun Alkalan kotun mai shari'a O-Gon Kwon ya ce alkalan kotun sun sami Radovan Karadzic da hannu cikin laifuffuka 10 cikin laifuffuka 11 da aka zarge shi da shi a gaban kotun da suka hada da kisan kiyashi tare da tilastawa al’umma barin gidajensu don haka kotun ta daure shi shekaru 40 a gidan zama.

Har ila yau kotun ta sami Mr. Karadzic dan shekaru 70 a duniya da hannu cikin kawanyar da aka yi wa garin Sarajevo daga watan Mayun 1992 zuwa Oktoban 1995 lamarin da share fagen kashe dubban mutanen garin.

Radovan Karadzic dai shi ne ya jagoranci sojojin Sabiya a kisan kiyashin da suka yi wa musulmi a yankin Srebrenica da ke karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1995, inda suka kashe musulmin yankin kimanin 8000, baya ga wasu dubban kuma da aka kashe a yayin yakin na Bosniya wanda aka bayyana shi da cewa shi ne ta'asa mafi muni da aka aikata a Turai tun bayan yakin duniya na biyu.