An Fara Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Kasar Rasha
(last modified Sun, 18 Mar 2018 16:14:07 GMT )
Mar 18, 2018 16:14 UTC
  • An Fara Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Kasar Rasha

Miliyoyin al'ummar kasar Rasha ne suka fito don kada kuri'arsu a zaben shugaban kasar da aka fara a yau din nan a zaben da ake ganin shugaban kasar mai ci Vladimir Putin ne zai lashe shi.

Rahotanni daga kasar Rashan sun bayyana tun da safiyar yau ne da misalin karfe 8 na safe agogon Rashan aka fara kada kuri'ar inda ake sa ran mutane miliyan 109 da suka cancanci kada kuri'a za su kada kuri'unsu a mazabu kimanin 94,500 a duk fadin kasa bugu da kari kan wasu 'yan kasar su 1.8 da suke rayuwa a kasashen waje da za su kada kuri'unsu a mazabu 369 don zaban sabon shugaban kasar.

Kuri'un jin ra'ayin al'umma da aka gudanar a kasar na nuni da cewa daga dukkan alamu shugaba Vladimir Putin ne zai lashe zaben don wa'adi na shida na shugabancin kasar inda ake sa ran zai kara da sauran 'yan takara bakwai wanda mafiya fice daga cikinsu  su ne hamshakin dan kasuwa din nan Pavel Grudinin; sai kuma tsohon dan jarida , Ksenia Sobchak; da kuma tsohon dan kishin kasa Vladimir Zhirinovsky.

A shekara ta 2000 ne aka fara zaban shugaba Putin dan shekaru 65 a matsayin shugaban kasar bayan da ya karshen mulki daga wajen tsohon shugaban kasar  Boris Yeltsin, wanda yayi murabus daga karagar mulkin watanni shida kafin wa'adin mulkinsa ya kare.