MDD Ta Damu Kan Halin Da Ake Ciki A DRC
Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana matukar damuwa sakamakon tabarbarewar yanayin da ake ciki a Jamhuriyar demokaradiyyar Kongo (DRC).
A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, kwamitin sulhun MDD ya kuma bayyana damuwa game da karuwar mutanen da rikicin ya tilasawa zama a sansanonin 'yan gudun hijira a kasar, wanda ya ninka har sau biyu idan aka kwatanta da shekarar bara wato ya zarta mutane miliyan 4.49.
Game da wannan batu, kwamitin sulhun MDD ya jaddada bukatar shawo kan matsalar kungiyoyin masu dauke da makamai dake cigaba da haifar da barazana ga zaman lafiyar kasar.
A game da hakan ne kwamitin yake bukatar a gudanar da sahihin zabe wanda zai kunshi dukkan bangarorin kasar, a matsayin wani muhimmin matakin da zai kawo dauwamamman zaman lafiya da kwanciyar hankali a DRC.
Haka zalika kuma kwamitin ya bayyana damuwa sakamakon karuwar tabarbarewar yanayin damar shigar da kayan tallafi a yankin gabashin DRC, sakamakon rashin tsaro da tashe-tashen hankula a yankin, da kuma cigaba da kaddamar da hare hare da ake yi kan jami'an bada agaji a yankin.