Kasar Iran Ta Kirayi Saudiyya Da Ta Kawo Karshen Yakin Yemen
(last modified Wed, 28 Mar 2018 16:09:54 GMT )
Mar 28, 2018 16:09 UTC
  • Kasar Iran Ta Kirayi Saudiyya Da Ta Kawo Karshen Yakin Yemen

Jakadan Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Gholamali Khoshrou, yayi watsi da zargin kasar Saudiyya na cewa Iran tana aikewa da makamai masu linzami kasar Yemen, yana mai kiranta da ta kawo karshen yakin da take yi a Yemen din da kuma zama teburin tattaunawa da makwabtanta.

Malam Gholamali Khoshrou ya bayyana hakan ne a matsayin mayar da martani ga wasikar da takwararsa na kasar Saudiyya, Abdullah al-Muallami, ya rubuta wa Kwamitin Tsaron MDD yana mai zargin Iran da ba wa dakarun 'yan Houthi na kasar Yemen makamai masu linzami masu cin dogon zango.

Jakadan na Iran ya ce shekaru uku kenan Saudiyya take ruwan bama-bamai a kan al'ummar Yemen ba tare ta cimma wata nasara ba in ban da zubar da jinin al'ummar Yemen da sanya su cikin mawuyacin hali na yunwa. Don haka yace maimaikon Saudiyya ta ci gaba da zargin wasu mutane na daban, kamata yayi da kawo karshen siyasarta na tsokana da haifar da yaki da kuma ci gaba da zubar da jinin al'ummar ta Yemen.

Mr.  Khoshrou ya ci gaba da cewa wannan ba shi ne karon farko da Saudiyya take irin wannan zargi a kan Iran ba don ta rufe irin shan kashin da take sha a Yemen din, don haka ya kirayi mahukuntan Saudiyya da su kawo karshen wannan yaki da kuma shiga tattaunawa hakan ita ce kawai mafita.

A shekaran jiya ne dai Saudiyya da kawayenta suka nuna wasu tarkacen wasu abubuwa da ta ce na makamai masu linzamin da Iran ta ke ba wa 'yan Houthin ne wadanda suka harba su cikin Saudiyyan a shekaran jiya.