Rasha Da China Suna Kara Karfafa Kawancensu A Bangaren Ayyukan Soji
(last modified Wed, 04 Apr 2018 05:49:15 GMT )
Apr 04, 2018 05:49 UTC
  • Rasha Da China Suna Kara Karfafa Kawancensu A Bangaren Ayyukan Soji

Wata babbar tawagar manyan hafsoshin sojin kasar China karkashin jagorancin ministan tsaron kasar ta China ta isa birnin Moscow na kasar Rasha.

Tashar pressTV ta bayar da rahoton cewa, bayan isar bababr tawagar manyan jami'an sojin kasar China a jiya a birnin Moscow na kasar Rasha a jiya, ministan tsaron kasar ta China Wei Fenghe ya bayyana cewa; zuwansu Rasha babban sako ne ga Amurka, domin ta san cewa Rasha da China kansu hade yake, kuma duk wata barazana a kan daya daga cikinsu, barazana ce gare su duka.

A nasa bangaren ministan tsaron kasar Rasha janar Sergei Shoigu a lokacin da yake tarbar takwaransa na China da kuma tawagarsa a jiya a birnin Moscow, ya bayyana kawancen China da Rasha da cewa kawance ne mai tsohon tarihi, kuma bangarorin biyu sun hada kai da juna domin tabbatar da tsaron kasashensu da kuma ci gaban al'ummominsu a dukkanin bangarori.

Kawancen Rasha da China dai na a matsayin abin da Amurka da kasashen turai ke kallonsa a matsayin babbar barazana a gare su, wanda hakan ke a matsayin babban karfen kafa ga manufofin siyasarsu a kan sauran al'ummomin duniya.