Koriya Ta Arewa Ta Wallafa Wani Faifan Bidiyon Wargaza Amurka
(last modified Sat, 26 Mar 2016 17:52:34 GMT )
Mar 26, 2016 17:52 UTC
  • shugaban koriya ta Arewa Pyongyang
    shugaban koriya ta Arewa Pyongyang

Yau Asabar kasar Koriya ta Arewa ta wallafa wani sabon faifan bidiyo farfaganda na kaiwa Amurka harin makamin nukiliya, tare da yiwa makofciyar ta koriya ta Kudi barazana harin soja saboda cin fuska ga shugaban ta Kim jong-un.

faifan bidiyon na muntina hudu mai suna '' damar karshe'' da shugaba Pyongyang ya wallafa a shafin internet ya nuna wani yadda aka harbo wani makamin nukiliya daga kasan ruwa ya ragargaza Washinton, sanan aka nuno tutar Amurka ya ci da wuta.

karshen film din kuma ya nuno wani makami mai cin dogon zango a sararin samaniya ya dawo kasa ya kuma tarwatse a dandalin Lincoln Memorial na tunawa da shugaban Amurka na 16, kafin daga bisani birnin ya yi raga-raga, sai kuma aka rufe da wani sako a rubuce dake cewa '' idan Amurka ta kusanto mu da kiris zamu ragargaza ta nan take da karfin makamin mu na nukiliya''.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da Koriya ta Arewa ke fitar da ire-iren wadanan faya-fayan bidiyo ba, inda ko a shekara 2013 ta fitar da wani makamacin sa inda wani maharbi yayi saiti da fadar wite house da kuma ragargaza birnin.

tun dai bayan gwajin makamin nukiliyar da koriya ta Arewa tayi al'amura suka dagule a yankin, inda ta ke ci gaba da harba makaman masu cin dogon zango duk kuwa da kakaba mata da takunkunmai masu tsauri da Amurka ta yi.