Wani Jirgin Soja Ya Fadi A Rasha
Wani jirgin soja samfarin Yak-130 ya fadi yayin dake gudanar da ayukan koyarwa a jahar Voronezh dake tsakiyar kasar.
Kamfanin dillancin Irna ya habarta cewa da misalin karfe 9:40 na safiyar yau alhamis ne, jirgin ya fadi a jahar ta Voronezh. kafin faduwar jirgin, matukin jirgin ya kira cibiyar tsaron jahar kuma ya shaida musu cewa jirgin ya samu matsalar na'ura,
Rahoton ya ce matukin jirgin da wanda yake koyawa tukin jirgin sun tsira da rayukansu.
Cikin wani kajeren labari da ta bayar tashar talabijin din Zvezda na ma'aikatar tsaron Rasha ta ce wadanda ke cikin jirgin da ya fadi sun yi tsira da rayukansu bayan da suka yi amfani da lamar tsira.
Ya zuwa yanzu gwamnatin ta Rasha ba tayi karin haske kan dalilin faduwar jirgin.