Harin Siriya : Tabas Akwai Abunda Zai Biyo Baya _ Rasha
Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce kawancen Amurka da Faransa da kuma Birtaniya ya harba makamai masu linzami sama da dari a kan kasar Siriya, saidai an kakkabo dayewa daga cikinsu.
Rasha dai ta yi gargadi akan abunda zai iya biyo baya, bayan harin kasashen uku.
Bayanan da Rashar ta fitar kafin sanarwar da zata fitar nan bada jimawa ba kan harin da aka kai kan Siriya, ta ce hare haren da kasashen yamma suka kai kan Siriya basu shafi sansanin sojin Rashar ba ko kuma yankunan da dakarunta ko makamman ke bada kariya ba a Siriya.
Rasha ta ce mafi yawan makaman garkuwanta na yankunan Tartous da Hmeimim ne.
Kafin hakan dai ma'aikatar harkokin wajen Rashar ta ce, Siriya data shafe shekaru tana jan daga daga barazanar 'yan ta'adda, ta fuskanci hare hare daga kasashen yamma a daidai lokacin da take da damar gina kanta da samun makoma mai kyau.