Isra'ila Ta Sallami Bakin Haure 'Yan Afrika 200
Sama da bakin haure 'yan Afrika, 200 ne da ake tsare da su a wani gidan yari dake kudancin H.K. Isra'ila aka sallama a jiya Lahadi.
Wannan dai ya biyo bayan umurnin da kotun kolin H.K. Isra'ilar ta bayar na sallamar bakin hauren, idan ba'a samu wata kasa ta daban data karbe su ba.
A watan Fabrairu da ya gabata ne mahukuntan yahudawan suka jefa bakin hauren da suka shiga Isra'ilar ba bisa ka'ida ba, a gidan kurkukun Saharonim.
A ranar Juma'a data gabata kasar Ruwanda ta sanar da anniyarta na karbar bakin hauren 'yan kasashen Sudan da Eritra kimanin 500 cikin kasarta.
Gwamnatin Benjamin Netanyahu na shirin korar dubban bakin haure 'yan Sudan da Eritra, wandanda suka shiga Isra'ilar ba bisa kai'da ba, bayan da ta yi musu tayin ba ko wanne daga cikin dalar Amurka 3,500 akan ya amunce koma wa kasarsa ko kuma a tusa keyarsa gidan kaso idan ya ki barin Isra'ilar.