Harin Sojin Birtaniya Kan Kasar Syria Ya Bar Baya Da Kura
Firayi minista ta kasar Birtaniya Theresa May na fuskantar kakkausar suka a majalisar dokokin kasar sakamakon yin gaban kanta da ta yi wajen bin sahun Amurka, domin kai wa kasar Syria harin soji ba tare da tuntubar majalisar dokokin kasar ba.
shugaban jam'iyyar Labour ta kasar Birtaniya Jeremy Corbyn ya bayyana matakin na Theresa May a matsayin raini ga majalisar dokokin Birtaniya, inda ya ce gwamnati ita kadai ba ta hakkin yanke hukunci kan daukar matakin yaki a wajen kasar Birtaniya ba tare da amincewar majalisar dokoki ba.
Ya kara da cewa; majalisar dokoki tana gaba da gwamnati, domin al'ummar Birtaniya suka zabi majalisar dokoki, ita kuma majalisa ta kafa gwamnati, a kan hakan majalisa ce kai tsaye take wakiltar al'ummar Birtaniya, yayin da ita kuma take wakiltar majalisa, a kan haka dole ne gwamnatin Theresa May ta zama mai biyayya ga majalisa, mai karbar umarni daga majalisar Birtaniya, ba daga Donald Trump ba.
Da dama daga cikin 'yan majalisar dokokin kasar ta Birtaniya dai sun nuna fushinsu matuka dangane da yadda May ta yi gaban kanta wajen kai wa kasar Syria hari tare da Amurka da Faransa, ba tare da iznin majalisa ba, kamar yadda dubban jama'a a birane daban-daban na kasar ta Birtaniya suka yi ta gudanar da zanga-zangar domin nuna kiyayyarsu da wannan mataki.