Apr 26, 2018 11:54 UTC
  • Sojojin Kasar Ukrai Kimani 500 Suka Kashe Kansu Da Kansu

Babban mai gabatan da kara na sojojin kasar Ukrai ya bada sanarwan cewa sojojin kasar 554 ne suka kashe kansu da kansu a yakin da kasar take fafatawa da yan tawaye a gabancin kasar.

Kamfanin dillancin labaran News ya nakalto Anatollii Matios babban mai gabatar da kara na sojojin Ukrai yana fadar haka, ya kuma kara da cewa sojojin kasar kimani dubu 326 suke fafatawa da yan tawaye a yankunan gabacin kasar ta Ukrai, amma banda asarorin rayuka wadanda yan tawayen suka haddasa a cikin sojojin kasar, wasu sojoji 554 sun kashe kansu da kansa tun lokacinda aka fara yakin, sannan wasu dubu 3,784 suka ji rauni. 

Matios ya kara da cewa saboda yawan kashe kai wanda sojojin suke yi wa kansu gwamnatin kasar a wannan shekara ta 2018 ta ware dalar Amurka milliyon 4 don samrawa sojojin taimakon likitoci wadanda suka kore a wannan fannin. 

Tags