Bakin Haure 5 Sun Hallaka A Gabar Tekun Aspaniya.
(last modified Thu, 26 Apr 2018 19:03:56 GMT )
Apr 26, 2018 19:03 UTC
  • Bakin Haure 5 Sun Hallaka A Gabar Tekun Aspaniya.

jami'an agajin ruwa na kasar Aspaniya sun sanar da mutuwar bakin haure biyar a gabar tekun ruwan kasar.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto jami'an agajin ruwan Aspaniya a wannan alhamis na cewa wani kwale-kwale dake dauke da bakin haure dake son shiga kasashen Turai ya tarwatse a gabar tekun ruwan kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar hudu daga cikinsu

Sanarwar ta ce mutum na biyar da ya rasa ransa daga cikinsu, ya mutu ne sanadiyar bugawar zuciya.

Jami'an kai agajin ruwa na kasar Aspaniyar sun bayyana a daren jiya laraba, jami'an tsaron ruwan sun yi nasarar tsabke bakin haure 54 dake cikin kwale-kwale biyu a yayin da suke kokarin shiga cikin kasar ta barauniyar hanya.

Bayan kasashen Italiya da Girka, kasar Aspaniya ita ce ta uku na bakin haure ke amfani da ita wajen shiga Turai.

Hukumar dake kula da 'yan gudun hijra ta MDD ta sanar da cewa daga farkon watan janairu zuwa 25 ga watan Maris din da ya gabata, bakin haure 120 suka hallaka a yayin da suke shiga kasar Aspaniya daga kasar Marocco.