Sama Da Bakin Haure 600 Ne Suka Hallaka A Tekum Bahrum
Hukumar dake kula da 'yan gudun hijra ta MDD ta sanar da mutuwar bakin haure sama da 600 a tekun Bahrum.
Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar Sin ya nakalto Joel Millman kakakin Hukumar dake kula da 'yan gudun hijra ta MDD daga birnin Ganeva na cewa daga farkon wannan shekara zuwar karshen watan Avrilun da ya gabata, bakin haure 606 suka hallaka a yayin da suke kokarin shiga cikin kasashen Turai ta barauniyar hanya a tekun Bahrum.
Mista Joel Millman ya kara da cewa daga cikinsu akwai 217 da suka hallaka a gabar ruwan Aspaniya.
Bisa wannan rahoto, daga farkon shekarar 2018 zuwa karshen watan Avrilu kimanin bakin haure dubu 22 ne suka shiga kasashen Turai, kuma idan aka kwatamta da na shekarar 2017 din da ta gabata, adadin ya ragu da kasa da rabi.