Amurka Ta Kara Dorawa Venezuela Takunkumai Na Tattalin Arziki.
Mataimakin shugaban kasar Amurka ya bada sanarwan dorawa yan kasuwan kasar Venezuela 3 da kuma wasu kamfanonin kasar 20.`
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Mike Pence yana fadar haka a jiya Litinin. Ya kuma kara da cewa takunkuman sun hada da mutane ukku ya kasuwa da kuma kamfanonin kasar ta Venezuela 20 don irin kusancinsu da shugaban kasa Nikolas Madoro .
Banda haka Mike Pence ya bukaci gwamnatin kasar ta dage zaben shugaban kasar da za'a gudanar a kasar a ranar 20 ga watan mayun da muke ciki.
Sai kuma a maida martanin da ya yi masa Shugaban kasar na Venezuela ya bayyana cewa wannan maganar ta Mike Pence wani shisshigi ne a cikin harkokin cikin gidan kasrsa, sannan yayi kira ga yan adawarsa kasar wadanda Mike Pence yake magana a madadinsu da su dawo kan teburin shawara don tattauna sabanin da ke tsakaninsu.