May 12, 2018 08:06 UTC
  • Priministan Kasar Britania Ta Zanta Da Shugaban Kasar Amurka Kan Janyewar Kasar Daga Yerjejeniyar Nukliyar Iran.

Primistan kasar Britania Theresa May ta tattauna ta wayar tarho tare da shugaban kasar Amurka Donal Trump kan tasirin da takunkuman da Amurkan zata dorawa Iran bayan ta janye daga yerjejeniyar shirin Nukliyar kasar Iran kan kamfanin Britania da sauran ayyukanta a kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran reuters yabayyana cewa Priministan kasar Britania ta bukaci sanin matsayin kamfanin kasashen turai dangane da takunkuman da Amurka zata sake dawo da su kan Iran. Labarin ya kara da cewa akwai tababa dangane da kasashe ukku na tarayyar Turai kan ci gama da rike alkawarinsu na aikin da yerjejeniyar. 

Tuni dai kasashen Faransa, Baritani da kuma Jamus wadanda suke cikin yerjejeniyar shirin Nukliyar kasar Iran, suka fara bayyana kalamai mai kama da na Trump na abinda suka kira rikita yankin gabas ta tsakiya wanda kasar Iran take yi. Da kuma shirinta na makamai masu linzami.

Iran dai ta bukaci kasashen ukku su fito fiki su aiwatar da yerjejeniyar shirin nukliyar kasar idan har da gaske duke nuna kan alkawarinsu na ci gaba da mutunta yerjejeniyar. 

Tags