Rasha: Ficewar Amurka Daga Yarjejeniyar Nukiliya Ya Kusanta Rasha Da Turai
Wani jami'in fadar Kremlin ta kasar Rasha Yuri Ushakov ya ce; An sami kusanci a tsakanin Rasha da turai saboda batun yarjejeniyar makamashin Nukiliya
Ushakov ya ci gaba da cewa; Shugaban Vladimir Putin da shugabar gwamnatin Jamus sun tattauna a ranar juma'a ta wayar tarho akan muhimmanci ci gaba da aiki da yarjejeniyar ta Nukiliya. Bugu da kari ya ce;Moscow da Berlin suna da matsaya guda daya akan batun na Nukiliya.
Jami'in na fadar Kremlin ya kuma bayyana yadda aka ci gaba da tattaunawa tsakanin shugaban kasar Rasha da kuma takwaransa na Faransa.
A gefe daya shugaban kwamitin kasa da kasa na majalisar kasar Rasha, ya fadi cewa; ya jaddada cewa;wajibi ne a sake tattauna batun yarjejeniyar ta Nukiliya a cikin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.