An Fara Zaben Shugaban Kasa A Kasar Venezuela
(last modified Sun, 20 May 2018 18:59:18 GMT )
May 20, 2018 18:59 UTC
  • An Fara Zaben Shugaban Kasa A Kasar Venezuela

A safiyar yau Lahadi ne aka fara zaben shugaban kasa a kasar Venezuela

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya bayyana cewa an bude rumfunan zabe ne tun misalin  karfe 6 na safiyar  yau 20 ga watan Mayu na shekara ta 2018. Sannan  mutane miliyon 20,500,000 ne suka cancanci kada kuri'a a wannan zaben. Har'ila yau za'a rufe rumfunan zabe ne da karfe 6 na yamma. 

A bangaren tsaro kuma gwamnatin kasar ta zuba yansanda dubu 300 a duk fadin kasar don tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin amince da zaman lafiya. 

A wannan zaben dai masu kada kuri'a zasu zabi shugaban kasa da kuma yan majalisar dokokin kasar. A bangaren yan takarar shugaban kasa kuma akwai yan takara 6, amma fitattu daga cikinsu su ne shugaban kasa mai ci Nicolas madoro da kuma abokin hamayyarsa Henry Falcon.

A tsarin mulkin kasar Venezuela dai shugaban kasa zai yi shekaru 6 ne a duk lokacinda aka zabe shi a kan kujerar shugabanciun kasar, sannan a cikin watan Jenerun shekara ta 2019 mai zuwa ne yakamata sabon zabebben shugaban kasa ya yi rantsuwar kama aiki.