An Fara Zaben Shugaban Kasa A Kasar Venezuela
A safiyar yau Lahadi ne aka fara zaben shugaban kasa a kasar Venezuela
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya bayyana cewa an bude rumfunan zabe ne tun misalin karfe 6 na safiyar yau 20 ga watan Mayu na shekara ta 2018. Sannan mutane miliyon 20,500,000 ne suka cancanci kada kuri'a a wannan zaben. Har'ila yau za'a rufe rumfunan zabe ne da karfe 6 na yamma.
A bangaren tsaro kuma gwamnatin kasar ta zuba yansanda dubu 300 a duk fadin kasar don tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin amince da zaman lafiya.
A wannan zaben dai masu kada kuri'a zasu zabi shugaban kasa da kuma yan majalisar dokokin kasar. A bangaren yan takarar shugaban kasa kuma akwai yan takara 6, amma fitattu daga cikinsu su ne shugaban kasa mai ci Nicolas madoro da kuma abokin hamayyarsa Henry Falcon.
A tsarin mulkin kasar Venezuela dai shugaban kasa zai yi shekaru 6 ne a duk lokacinda aka zabe shi a kan kujerar shugabanciun kasar, sannan a cikin watan Jenerun shekara ta 2019 mai zuwa ne yakamata sabon zabebben shugaban kasa ya yi rantsuwar kama aiki.