Yau Duniya Ke Bikin Ranar Dakarun Wanzar Da Zaman Lafiya
(last modified Tue, 29 May 2018 18:59:22 GMT )
May 29, 2018 18:59 UTC
  • Yau Duniya Ke Bikin Ranar Dakarun Wanzar Da Zaman Lafiya

Saktare janar na MDD Antonio Guterres ya bayyana dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD a matsayin jari na tabbatar da sulhu da tsaro a duniya

Cikin wani jawabi da ya gabatar a wannan rana da duniya ke tuni da ranar dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD, saktare janar na majalisar Antonio Guterres ya ce a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 1948 ne Kwamitin tsaro MDD ya amince da ayyukan kare sulhu na Majalisar a yankin gabas ta tsakiya.sannan kuma ya yabawa dakarun da suka bayar da rayukansu domin ceto milyoyin mutane a duniya

Har ila Mista Antonio Guterres ya dauki alkawarin inganta ayyukan dakarun wanzan da zaman lafiya na Majalisar dinkin Duniya.

Babban saktaren MDD ya ce majalisar ta dauki alkawarin karfafa ayyukan dakarunta, musaman ma wajen horo na musaman na kare hakkokin bil-adama da kuma mutunta Mata idan aka la'akari da zargin da ake yi musu na cin zarafin  mata  a yayin da suke gudanar da ayyukansu.