Nicky Haley: Manufar Hamas Kawo Karshen Isra'ila
(last modified Thu, 31 May 2018 06:44:44 GMT )
May 31, 2018 06:44 UTC
  • Nicky Haley: Manufar Hamas Kawo Karshen Isra'ila

Wakiliyar Amurka a MDD Nicky Haley da take nuna fishin fadar White House da ta kasa samar da kudiri kan kungiyar gwagwarmayar Palastinawa na cewa tushen manufar kungiyar Hamas kawo karshen Isra'ila.

A daren talatar da ta gabata wakiliyar Amurka a MDD ta bukaci gudanar da zaman gaggauwa a kwamitin tsaro na Majalisar domin daukan mataki kan kungiyar Hamas da ta halba rokoki zuwa haramtacciyar kasar Isra'ila.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto Nicky Haley a marecen jiya Laraba yayin zaman kwamitin tsaron MDD na cewa a ranar talatar da ta gabata akalla kungiyar gwagwarmayar Hamas ta Palatinu ta halba rokoki 70 zuwa ga HKI, kuma idan aka yi la'akari da ya wuraren da ta harba wadannan rokoki, tana nufin cutarwa da kuma kawo karshen Isra'ila.

A daren Talatar da ta gabata ce dakarun Isra'ila suka kaddamar da hare-hare kan wuraren dakarun gwagwamarya na Palastinu a yankin Zirin Gaza, a matsayin mayar da martani, dakarun gwagwarmayar sun yi ruwar rokoki kan kauyukan yahudawa 'yan kama wuri zauna, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar wasu sojojin Isra'ila.

Wannan goyon baya da Amurka ke bawa Isra'ila na zuwa ne a yayin da Isra'ila ta kashe Palastinawa sama da 120 tare da jikkata saman da dubu 13 a kasa da wata guda.