Amurka Na Kara Matsin Lamba Akan Kasar Pakistan
https://parstoday.ir/ha/news/world-i32139-amurka_na_kara_matsin_lamba_akan_kasar_pakistan
Jakadiyar Amurka a MDD Nikki Haley ta ce kasarta tana kara matsin lamba akan kasar Pakistan
(last modified 2018-08-22T11:32:03+00:00 )
Jun 30, 2018 11:07 UTC
  • Amurka Na Kara Matsin Lamba Akan Kasar Pakistan

Jakadiyar Amurka a MDD Nikki Haley ta ce kasarta tana kara matsin lamba akan kasar Pakistan

Nikki Haley ta kara da cewa Amurka na yin matsin lambar ne akan kasar Pakistan saboda mafakar da take bai wa 'yan ta'adda, tare da bayyana fatan hakan zai yi tasiri.

Jakadiyar ta Amurka a MDD ta ci gaba da cewa; Siyasar Amurka akan kasar Afghanistan ita ce, Pakistan ce mafi girman tarihi, don haka take yi mata matsin lamba ko za ta sauya halinta.

Sai dai Pakistan ta bayyana cewa; Abin da Amurka take yi shi ne kokarin ficewa daga kasar Afghanistan amma tana neman dorawa Pakistan kashin da ta sha ne a cikin kasar ta Afghnaistan.