Russia 2018 : Rasha Ta Tsallake Zuwa Kwata-final
Kasar Rasha mai karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, ta tsallake zuwa zagayen kusa da dab da karshe bayan ta samu nasara kan Spain a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
An tafi bugun fanareti ne bayan karshen wasan 1-1 a mintina 120 da aka shafe ana fafatawa, a inda mai tsaron ragar Rasha Igor Akinfeev ya kabe kwallayen biyu na Spain.
Wannan shi ne karon farko da Rasha ta kai a zagayen kwata final, a tarihin cin kofin kwallon kafa na duniya, a yayin da kuma shi ne karo na biyu a jere da Spain ta kasa tsallake wa zuwa zagayen kusa da dab da karshe (2014-2018).
Spain yanzu ta bi sahun manyan kasashen da aka fitar a gasar da suka hada da Jamus mai rike da kofin gasar da Argentina da Portugal.
A yanzu dai ana cikin karawa tsakanin Denmark da Croatia, wadanda daya daga cikinsu ne, Rasha za ta hadu da ita a zagayen kusa da dab da karshe.